Cibiyar kula da girgizar kasa ta kasar Sin ta bayyana cewa, girgizar kasar ta aukuwa yankin Jiuzhaigou ne da misalin karfe 9.19 na dare agogon kasar Sin, kuma zurfinta ya kai kilomita 20.
Mahukuntan kasar Sin dai sun yi kiran da a dauki dukkan matakan da suka dace na samar da agaji da aikin ceto ga wadanda lamarin ya shafa.
Ma'aikatan agaji na taimakawa masu yawon bude ido da suka makale a wurin yawon shakata mai korama da jama'a ke son ziyararta na Jiazhaigou. Yanzu haka hukumomin sun riga sun kwashe sama da masu yawon shakatawa 45,000, domin sake musu matsuguni.
Hedkwatar rage radadin girgizar kasa ta lardin ta bayyana cewa, sama da ma'aikata 800 ne suke karade kauyuka don neman wadanda suka makale sakamakon wannan bala'i.(Ibrahim)