An sanya wa tauraron sunansa ne daga sunan wani masani mai suna Zhang Heng, wanda ya rayu yayin daular Han ta gabashi da ta yi mulki tsakanin shekarun 25 zuwa 220. Mr. Zhang Heng dai shi ne masani na farko da ya gudanar da nazari, tare da kirkiro magwajin auna girgizar kasa irin sa na farko a shekara ta 132.
Ana sa ran tauraron Zhangheng 1 zai rika tattara bayanai da suka kai magwajin lamba ta 6 ta girgizar kasa a kasar Sin, da kuma magwajin da ya haura lamba 7 a sauran kasashen duniya, tare da kimanta motsi da ake samu mai nasaba da girgizar kasa.