in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta fara gina cibiyoyin bibiyar hasashen girgizar kasar
2018-05-08 12:51:07 cri

Kasar Sin za ta fara gina cibiyoyin sa ido a yankunan da ka iya fuskantar girgizar kasa, a wani yunkuri na fadada hasashen girgizar kasa.

A cewar Wang Tun, daraktan cibiyar rage aukuwar iftila'i ta Institute of Care-Life ta kasar Sin dake da mazauni a Chengdu, babban birnin lardin Sichuan, bisa shirin da aka yi, za a gina cibiyoyin sa ido 2,000 cikin shekaru 2, a lardunan 2 da sufa fi fuskantar barazanar girgizar kasa, wadanda suka hada da Sichuan da Yunan dake kudu maso yammacin kasar Sin.

Wang Tun ya ce, za a kafa na'urorin aikewa da bayanai a dukkan cibiyoyin, ta yadda za su rika tattaro bayanai na nauyi da karfin dake kilomita 8 zuwa 20 na karkashin kasa, da nufin samarwa masu bincike bayanai game da hasashen girgizar kasa.

Manufar wannan aikin ita ce, samun nasarar gudanar da hasashen girgizar kasa, wadda ke farawa daga nisan kilomita 20 dake tsakanin ban kasa da karkashin kasa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China