in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD ya jaddada mahimmancin dakile zirga zirgar 'yan ta'adda
2019-05-08 11:08:58 cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya jaddada muhimmancin hana zirga-zirgar 'yan ta'adda.

A shekaru 7 da suka gabata, an sha fama da yawaitar zirga-zirgar 'yan ta'adda tsakanin shiyyoyin duniya. A cikin shekaru biyu kacal da suka gabata, sama da mayakan 'yan ta'adda dubu 40 'yan kasashen waje daga kasashen duniya sama da 110 ne aka kiyasta sun yi bulaguro domin shiga kungiyoyin ta'addanci a kasashen Syria da Iraqi, in ji mista Guterres, a lokacin da yake kaddamar da shirin dakile zirga-zirgar mayakan 'yan ta'adda.

Tun bayan samun galaba kan mayakan kungiyar IS, mayakan 'yan ta'adda da dama suke ta kokarin komawa gidajensu ko sauya sabbin wuraren zama domin samun tsira ko kuma shiga sauran sassan duniya masu fama da tashe tashen hankula, in ji jami'in MDDr.

Ganowa tare da dakile duk wani shirin mayakan 'yan ta'adda da sauran bata gari tun gabanin su kaddamar da hare-hare su ne abubuwan da suka fi dacewa a baiwa fifiko a tsakanin kasa da kasa, in ji Guterres. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China