A jawabinsa yayin bikin, babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya ce, bayyana nagartar alakar kasashen duniya kadai ba zai isa ba, dole ne a tabbatar da fa'idar alakar, a kuma nunawa duniya cewa, alakar za ta iya warware matsalolin da duniya ke fuskata da dunkulewar duniya cikin daidaito da kowa zai amfana.
Jami'in na MDD ya ce, kawancen kasashe da aka kafa a shekarar 1919, wata alama ce dake nuna wanzuwar sabon tsarin alakar diflomasiyyar kasashen duniya, wadda cikin sama da shekaru 100 da suka gabata, ta bunkasa daga matakin farko na kawance zuwa aiki mai sarkakiya kuma cikakken da MDD take gudanarwa a halin yanzu.(Ibrahim)