Wu ya ce a halin da ake ciki, yankin Darfur yana da matukar muhimmanci ga wanzuwar zaman lafiya a Sudan, kuma akwai bukatar daga matsayinsa daga yanayin wanzar da zaman lafiya zuwa sake gina kyakkyawan yanayi na kwanciyar hankali.
Ya ce ya kamata kasashen duniya su ci gaba da aiwatar da matakan siyasa, da na wanzar da zaman lafiya, domin cimma burin daidaita al'amura sannu a hankali, har a kai ga mika mulki ga farar hula lami lafiya ba tare da amfani da karfin soja a kasar ta Sudan ba. Kana a yi hadin gwiwar wanzar da zaman lafiya da tsaro a yankin Darfur mai fuskantar ayyukan 'yan aware. (Saminu Hassan)