in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yabawa gudunmuwar da tsiron Miracle Grass na kasar Sin ya bayar ga samun ci gaba mai dorewa
2019-04-19 10:46:36 cri
Shugabar babban zauren MDD Maria Fernanda Espinosa Garces, ta yabawa gudunmuwar da fasahar Juncao ta kasar Sin da ake wa lakabi da "miracle grass" wato tsiro mai ban al'ajabi ya bayar ga muradun samar da ci gaba masu dorewa.

A jawabinta na bude taron manyan jami'ai kan fasahar Juncao, Maria Espinosa ta ce ta yi farin cikin samun labarin cewa fasahar Juncao ta zama tambarin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya.

Ta ce fasahar na bada muhimmiyar gudunmuwa ga maradun ci gaba masu dorewa da ake son cimmawa ya zuwa 2030, da suka hada da yaki da talauci da samar da makamashi mai tsafta da daidaiton jinsi da raya muhallin halittu.

Juncao wadda ke nufin tsiron magani dake samar da lemar kwadi da ake iya ci, ya haifar da sakamako mai ban al'ajabi ga masana kimiyyar kasar Sin, wadanda suke nomansa domin samar da lemar kwadi mai magani wanda kuma za a iya ci, ko koma a ciyar da dabbobin gida tare kuma da zama shingen dake kare tuddan rairayi daga motsawa.

Maria Espinosa, ta ce a kananan tsibirai, Juncao na inganta jure sauyin yanayi tare da taimakawa wajen yaki da lalacewar filaye ta hanyar samar da abinci ga dabbobi da rage zaizayar kasa.

Ta kuma bayyana cewa, fasahar na kawo sauyi a wuraren da suka fi dacewa, ga rayuwar manoma da mata da yara da mutane masu bukata ta musammam. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China