in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon kasar Sin: Wajibi ne kasashen duniya su hada gwiwa wajen raya ayyukan wanzar da zaman lafiya
2019-05-08 09:49:42 cri
Wakilin din-din-din na kasar Sin a MDD Ma Zhouxu, ya bayyana cewa, wabiji ne kasashe da yankuna da ma daukacin kasashen duniya, su karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu, yayin da ake kokarin kafa dakarun wanzar da zaman lafiya.

Jami'in wanda ya shaidawa zaman muhawarar kwamitin sulhun MDD a bainar jama'a game da "zuba jari a bangaren zaman lafiya: samar da horo da dakarun da suka dace don inganta tsaro da kwazon ma'aikatan dake aikin wanzar da zaman lafiya", ya ce, wabiji ne a zage damtse wajen shiga hadin gwiwar samar da kwarewa ga aikin wanzar da zaman lafiya. Haka kuma ya kamata kasashe da yankuna da ma kasa da kasa su bunkasa alaka a tsakaninsu yayin da ake samar da ma'aikatan dake aikin kiyaye zaman lafiya.

Ya kara da cewa, wajibi ne a taimakawa kungiyar tarayyar Afirka (AU) da kungiyar ASEAN da sauran kugiyoyin shiyya-shiyya, a kokarin da suke yi na kara karfin dakarunsu dake aikin kiyaye zaman lafiya.

Wakilin na kasar Sin ya ce, ya zama tilas a dora muhimmanci tare da taimakawa rawar da AU da sauran manya da kananan kungiyoyin shiyya-shiyya ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Afirka, da taimakawa AU a kokarin da take yi na kafa rundunar kota-kwana da kai daukin gaggawa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China