Mai magana da yawun hukumar ta UNHCR Babar Baloch, ya shaidawa taron manema labarai cewa, gwamnatin Mozambique da hukumar ta UNHCR da sauran abokan hulda, sun fara mayar da iyalan da mahaukaciyar guguwar Idai ta raba da muhallansu zuwa wasu yankunan dake kusa da gidajensu na asali.
Baloch ya ce, suna fatan, nan da kwanaki 10 masu zuwa, kimanin mutane 700 za su bar sansanonin wucin gadi da suka hada da makarantu, dakunan taron jama'a, da dakunan karatu da sauran gine-gine da suka shafe sama da wata guda suka zaune.
A tsakiyar watan Maris din da ya gabata ne dai, mahaukaciyar guguwar Idai mai tafe ta ruwan sama, ta shafi kasashe kudancin Afirka da suka hada da Mozambique da Malawai, da kuma Zimbabwe. (Ibrahim)