in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi gargadi game da karuwar kyamar baki, inda kuma ta yabawa farfadowar Rwanda bayan kisan kiyashin kasar da ya cika shekaru 25
2019-04-13 16:32:37 cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi gargadi game da karuwar kyamar baki, yayin taron tunawa da cika shekaru 25 da kisan kiyashin kasar Rwanda, inda ya yabawa nasarorin da kasar ta samu bayan wannan iftila'in.

A Ranar 7 ga watan Afrilun 1994 ne aka fara kisan kiyashi a Rwanda, lamarin da ya shafe tsawon kwanaki 100, har zuwa tsakiyar watan Yulin shekarar, tare da yin sanadin rayukan mutane sama da miliyan 1, galibi 'yan kabilar Tutsi.

A shekarar 2003 ne, babban zauren MDD ya ayyana 7 ga watan Afrilun kowacce shekara, a matsayin ranar tunawa da kisan kiyashin da aka yi wa 'yan kabilar Tutsi a Rwanda a shekarar 1994. A bara ne kuma, zauren majalisar ya sauya lakabin da aka yi wa ranar zuwa Ranar tunawa da kisan kiyashin 1994 na Rwanda, yana mai tunatar da cewa, an kashe 'yan kabilar Hutu da wasu da suka nuna adawa da kisan kiyashin.

Yayin taron, Antonio Guterres ya yi kira ga shugabannin siyasa da na addinai da na kungiyoyin al'umma, su kauracewa jawaban kiyayya da nuna wariya, tare da yin aiki tukuru wajen magance tushen matsalolin dake barazana ga hadin kan al'umma, wadanda ke haifar da kiyayya da rashin hakuri da juna. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China