in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta dauki tsoffin malamai aiki a makarantun yankunan karkara
2019-05-04 15:59:05 cri
A wani yunkuri na inganta ilimi a yankunan karkara, gwamnatin kasar Sin na shirin daukar tsoffin malamai 4,000, domin bayar da darasi a makarantun yankunan karkara, a zangon karatu na 2019/2020.

Sanarwar da ma'aikatar ilimi ta kasar ta fitar, ta ce za a bude shirin mai taken "Silver Age" ne ga tsoffin shugabannin makarantun Firamare da malamai 'yan kasa da shekaru 65.

Ta ce malaman za su yi aiki ne na a kalla shekara 1, sannan za a karfafawa wadanda suka ci tantancewar da za a yi musu, gwiwar ci gaba da koyarwa.

Baya ga bayar da darasi, za kuma su iya tantance ayyukan sauran malamai, da gudanar da lakca ko taron bita domin kara wayarwa da malamai kai da taimakawa makarantu inganta ayyukansu.

A cewar wata kididdiga a hukumance, kasar Sin na da sama da malamai miliyan 2.9 a yankunan karkara ya zuwa karshen 2018. Hukumomin kula da ilimi sun kara himmantuwa wajen bunkasa raya ilimi a yankunan karkara da kuma inganta kimar malaman yankunan.

A shekarar 2018, malamai 1,800 da suka yi ritaya cikin koshin lafiya ne suka yi rejistar koyarwa a makarantun karkara. Yayin da larduna 19 suka tura malamai 4,000 domin su taimakawa aikin raya ilimi a yankunan Tibet da Xinjiang. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China