Rahoton ya ce, kasafin kudin da gwamnati ta warewa a bangaren Ilimi, ya kai sama da Yuan triliyan 3.6, adadin da ya karu da kaso 8.13 cikin 100 kan na shekarar da ta gabata.
Bugu da kari, rahoton ya nuna cewa, kusan rabin kudaden da aka kashe ya karkata ne ga bangaren samar da ilimi tilas, sai bangaren ilimin manyan makarantu, wanda ya kasance na biyu mafi girma tsakanin dukkan sassan Ilimin kasar. (Ibrahim)