Majalisar gudanarwar kasar Sin, ta fitar da shirin yi wa aikin koyar da ilmin sana'a gyaran fuska, inda ta ce, nan da shekarar 2020, kasar Sin za ta kafa rukunonin gwaji na koyar da ilmin sana'a guda 300, inda ta ke fatan kamfanoni matsakaita da kanana za su shiga aikin.
Kana ya zuwa shekarar 2022, za a kafa jami'o'in koyar da ilmin sana'o'i guda 50 a nan kasar Sin, ta yadda ma'aunin tsarin koyar da ilmin sana'a a kasar, zai kai sahun gaba a fadin duniya.(Jamila)