Chen Baosheng, ya bayyana haka ne a wani taro da aka yi kan shirye shiryen rage fatara a bangaren ilimi, wanda ya gudana lardin Yunnan.
Ministan ya yi kira ga jami'o'i da cibiyoyin ilimi dake cikin shirye-shiryen, su mayar da hankali kan manyan matsaloli, su kuma bullo da matakan da za su magance su, tare da yin aiki bisa kwarewa.
Ya ce ya kamata bayanai game da matakan tabbatar da samun ilimin da ya zama na dole na shekaru 9 da takaita yawan masu barin makaranta a yankuna masu fama da talauci da kuma yanayi da adadin yaran da suka isa zuwa makaranta a gidaje matalauta, su kasance bisa sanin cikakken yanayin da ake ciki.
Ya kuma bukaci a zabi jami'an da suka kware domin gudanar da shirye shiryen.
Har ila yau, ya ce ana bukatar karfafa sa ido domin tabbatar da samun sahihan sakamako daga shirye-shiryen. (Fa'iza Msutapha)