in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta fitar da tsare tsaren bunkasa ilimi a yankuna matalauta
2019-03-18 10:43:12 cri

Gwamnatin kasar Sin ta fitar da wasu tsare tsare, na inganta koyarwa a makarantun dake yankuna masu fama da talauci, ciki hadda samar da ingantattun kayayyakin koyarwa na zamani, da baiwa malamai horo na musamman domin inganta koyarwa.

Ma'aikatar ilimin kasar, ta ce za ta gudanar da ayyukan ba da horo ga jagororin makarantun firamare, da na kananan makarantun sakandare a irin wadannan yankuna.

Har wa yau, ma'aikatar za ta ba da tallafin na'urorin zamani na bunkasa ayyukan koyarwa. Cikin wadannan na'urori hadda wayoyin salula kusan miliyan guda, masu kunshe da manhajojin koyon harshen Sinanci da za a raba.

Bugu da kari, jami'ar koyon ilimi daga gida ta kasar, ita ma za ta samar da tsarin karbar darussa kusan 40 ta yanar gizo, ga daliban yankunan dake fama da talauci.

Yayin da dalibai ke amfana daga wadannan dabaru na inganta koyo ta yanar gizo, su ma shugabanni dake lura da sashen ilimi na irin wadannan yakuna, za su samu horo a fannin jagoranci, wanda zai ba su damar fadada gajiyar da ake fatan samu daga dabarun.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China