in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta sake samar da kayayyakin koyon Sinanci masu murya ga daliban firamare da sakandare
2018-12-23 16:46:21 cri

A yau Lahadi, babban gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin CMG da ma'aikatar ilmantarwa ta kasar, da kwamitin kula da harkokin yarukan kasar Sin sun sake shirya wani bikin samar da kayayyakin koyon Sinanci masu murya a nan Beijing. Wadannan kayayyakin koyon Sinanci masu murya da za a samarwa daliban firamare da sakandare na kasar na kunshe da bayanai 100.

An samar da irin wadannan kayayyakin koyon Sinanci masu muryoyi ne ba ma kawai ana kokarin yada harshen Sinanci ta hanyoyin sauti ba ne, har ma ana kokarin yada al'adun al'ummomin Sinawa, ta yadda daliban firamare da na sakandare za su iya samun cikakken imani ga al'adun kasar, kuma za a iya bunkasa karfin kasar Sin bisa al'adunta. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China