in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsarin amfani da makamashi a kasar Sin na kara kyautatuwa
2019-05-04 15:35:34 cri
Kasar Sin ta samu kyautatuwar tsarin amfani da makamashi a bara, inda aka samu karuwar amfani da makamashi mai tsafta.

Rahoton cibiyar shirya tsare-tsaren wutar lantarki da aikin injiniya ta kasar Sin, ya ce amfani da makamshi mai tsafta da ya hada da iskar gas da makamashin ruwa da na nukiliya da na iska, ya kai kaso 22.1 na yawan makamashin da aka yi amfani da shi a bara, adadin da ya karu da kaso 1.3 a kan na 2017.

Yawan amfani da kwal kuwa ya kai kaso 59 na jimilar makamashin da aka yi amfani da shi a bara, wanda ya ragu da kaso 1.4 a kan na 2017.

Jimilar makamashin da aka yi amfani da shi ya kai kwatankwacin ton biliyan 4.46 na kwal, wanda ya karu da kaso 3.3, karuwa mafi sauri da aka samu tun bayan 2014.

Rahoton ya kuma yi hasashen cewa, a bana ma, za a ci gaba da samun kyautatuwar tsarin amfani da makamashi da kuma makamashi mai tsafta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China