Yayin zaman majalisar zartarwar kasar da firaminista Li Keqiang ya jagoranta jiya Laraba, an yanke shawarar kafawa da fadada hanyoyin samar da iskar gas da zai hade kafofin da kasar ke samun makamashi daga cikin gida zuwa kasashen waje, ciki har da inganta na'urorin adanawa da jigilar makamashin.
Wata muhimmiyar takarda da aka fitar bayan ganawar, ta bayyana cewa, za a kara daukar matakan karfafa zuba jari a bangaren hako iskar gas da inganta yadda za a mayar da albarkatun da aka hako zuwa ga tsari na kasuwanci.
A hannu guda kuma mahukuntan kasar Sin sun lashi takwabin daidaita yadda ake samar da makamashi a lokacin zafi, musamman ta yadda za a biya bukatun mazauna manyan garuruwa da yankunan dake fama da gurbatar muhalli da suka dogara kan makamashi mai tsafta don maye gurbin kwal. (Ibrahim Yaya)