in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: Kasuwar ababen hawa masu amfani da sabbin makamashi na kara bunkasa
2019-03-11 21:23:36 cri

Sashen kerawa, da cinikayyar ababen hawa masu amfani da sabbin makamashi ta kasar Sin na kara bunkasa, inda a watan da ya gabata, kasuwar wadannan nau'o'in ababen hawa ta samu karin tagomashi, duk da tafiyar hawainiya da sashen cinikayyar ababen hawa ke fuskanta.

A cewar kungiyar kamfanonin kera ababen hawa ta kasar CAAM, a watan na Fabrairu, yawan wannan nau'i na ababen hawa da aka sayar a fadin kasar ya kai 52,900, adadin da ya karu da kaso 53.6 bisa dari a tsakanin shekara guda. A hannu guda kuma, sashen kirar wadannan nau'o'i na ababen hawa ya kara fadada da kusan sama da kaso 50 bisa dari.

Rahotanni na cewa, kasar Sin ta fadada kwazon ta, wajen yayata manufar amfani da wannan nau'o'i na ababen hawa, domin inganta kare muhalli, inda aka dauke haraji, da rage shi kan wasu motoci masu amfani da makamashi mai tsafta.

Kaza lika gwamnatin kasar na karfafa gwiwar kamfanonin kirar motoci, da su bude karin kamfanonin kera wadannan nau'o'in motoci, da kara inganta fasahohin su.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China