in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi amfani sosai da makamshi mai tsafta a 2018
2019-01-29 12:34:51 cri

Kasar Sin ba ta lalata makamashi mai tsafta da yawa ba a shekarar da ta gabata, yayin da ake tsaka da samun karuwar amfani da shi.

Babban jami'in ma'aikatar kula da makamashi na kasar Li Chuangjun, ya ce matsakaicin matakin kasar na amfani da karfin ruwa wajen samar da lantarki ya tsaya ne kan kaso 95 a shekarar 2018, yayin da raguwar amfani da karfin iska ya sauka da kaso 5, inda na karfin haske ya sauka da kaso 2.8.

A shekarar 2018, ma'aikatar da sauran sassan dake da alakata da ita, sun gyara wasu dabarun magance raguwar tallafi da karuwar lalata makamashin haske da saurin fadadar bangaren makamashin hasken ke haifarwa.

Kiddiddigar ma'aikatar ta nuna cewa, ya zuwa karshen shekarar 2018, makamashi mai tsafta na kasar Sin ya kai karfin sa'o'in kilowatt miliyan 728, wanda ya karu da kaso 12 bisa dari kan na bara.

Makamashin mai tsaftan ya samar da wutar lantarki mai karfin sa'o'i kilowatt trilliyan 1.87 a shekarar 2018, adadin da ya karu da kilowatt biliyan 170 daga shekarar da ta gabata. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China