in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta gina tsarin samar da makamashi mai tsafta ta hanyar kwal mafi girma a duniya
2019-02-12 21:02:19 cri

Hukumar kula da makamashi ta kasar Sin (NEA) ta bayyana cewa, kasar ta gina wani tsarin samar da makamashi mai tsafta ta hanyar amfani da kwal mafi girma a duniya. Wannan wani sabon mataki ne na rage abubuwa masu gurbata muhalli da tsimin makamashi da kasar ta bullo da shi

Hukumar ta NEA ta kuma bayyana cewa, kasar Sin ta ma dara mizanin abubuwan masu gurbata muhalli da take cimma da tsimin makamashi da gyare-gyaren da ake fatan aiwatarwa cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 13 na shekaru biyu a nan gaba.

Alkaluman hukumar na nuna cewa, ya zuwa karshen rubu'i na uku na shekarar 2018, karfin injunan samar da makamashin kasar bisa kwal wadanda ba sa gurbata muhalli ya kai sama da kilowatts miliyan 750 na hasken wutar lantarki, adadin da ya kai sama da kaso 75 na injunan samar da wutar lantarki bisa kwal da kasar ke da su.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China