in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta gaggauta aiwatar da manufar amfani da ababen hawa masu aiki da methanol
2019-03-20 13:18:34 cri

Mahukuntan kasar Sin, sun bayyana aniyar su ta gaggauta aiwatar da manufonin da za su kai ga bunkasa amfani da ababen hawa masu amfani da makamashin methanol.

Gwamnatin kasar dai ta fitar da ka'idojin aiwatar da wannan manufa ne a ranar Talata, ciki hadda gina tsarin samar da ababen hawa, da na tabbatar da nasarar kasuwar su.

Kaza lika akwai tsarin karfafa gwiwar kamfanonin dake kera ababen hawan, ta yadda za su daga matsayin fasahohin su, don dacewa da wannan sabuwar manufa. Ka'idojin aiwatar da manufar dai na hadin gwiwar ma'aikatar raya masana'antu da ta fasahar zamani, da kuma hukumar aiwatar manufofin ci gaba da gudanar da sauye sauye ne.

Takardun bayanin ka'idojin sun nuna cewa, Sin za ta gaggauta gina cikakken tsarin amfani da ababen hawa masu amfani da methanol, za ta kuma tallafa wajen tsara ayyukan masana'antu, da kungiyoyin da za su sauke wannan nauyi, ta yadda hakan zai dace da mataki na inganci, da matsayi na kasa da kasa.

Har ila yau, Sin za ta goyi bayan samarwa, da amfani da motoci masu iya amfani da makamashin methanol sanfurin M100 a lardunan Shanxi, da Guizhou, da Gansu, wuraren dake da tarin wannan sinadari na makamashi, kuma tuni aka fara gwada wannan fasaha.

Yawan sinadarin makamashi na methanol a kasar Sin tsakanin watannin Janairun zuwa Nuwambar bara, ya kai tan miliyan 43.14, bisa alkaluma da hukumar MIIT ta fitar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China