Mataimakin kwamandan da ya tsara rokar, Jin Xin shi ne ya bayyana hakan a farkon wannan shekara, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a hukumar kimiyar sararin samaniya da fasahar kere-kere ta kasar Sin. Yana mai cewa, za a harba roka ta farko a kan teku ne a tsakiyar wannan shekara a Rawayan Teku.
Ya ce, fasahar harba rokar a kan teku, zai taimakawa kasar Sin samar da hidimar harba rokoki ga kasashen dake cikin shawarar "ziri daya da hanya daya".
Tsayin rokar ta Long March -11 ya kai mita 20.8, kana nauyinta zai kai kimanin tan 57.6 a lokacin da ya tashi, kuma ita ce rokar dake amfani da farfeloli cikin sabbin rokoki dakon kaya na kasar Sin. Haka kuma ba ta da wani sarkakiya, za kuma a iya harba ta cikin kankanin lokaci.
Rokar ta Long March-11 wadda aka fara harba ta a ranar 25 ga watan Satumban shekarar 2015, ya zuwa yanzu ta yi dakon taurarin dan Adam 25 zuwa sararin samaniya a lokuta guda 6 kuma cikin nasara. (Ibrahim)