An harba tauraron ne mai lakabin Tianlian II-01, ta rokar Long March-3B, daga tashar harba tauraron dan Adam ta Xichang dake lardin Sichuan, da misalin karfe 12 saura mintuna 9 na dare bisa agogin birnin Beijing.
An tsara cewa, tauraron wanda shi ne irinsa na farko a jerin taurarin dake da matsayin fasaha a mataki na biyu, zai rika samar da bayanai, da auna su tare da sarrafa su, ya kuma ba da hidimomin sadarwa ga na'urorin sama jannati, da taurarin dan Adam, da rokoki da sauran wasu na'urori dake aiki a doron kasa. Tianlian II zai yi aiki sama na sauran takwarorin sa dake da matsayin fasaha a mataki na farko, kamar tauraron dan Adam na Tianlian I.
Ayyukan tauraron wanda zai samar da hidima mai sauri, ta musayar bayanai, da hidimomin sadarwa, za su kuma taimaka wajen bunkasa saurin isar da sakwanni, da tsaron na'urorin sama jannati, da saukaka ayyukan taurarin dan Adam, da rokokin dake jigilar bil Adam.
Wannan ne karo na 301 da aka yi amfani da rokar Long March wajen harba taurarin dan Adam. (Saminu Hassan)