in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta karbi bakuncin taron kolin raya fasahohin zamani karo na biyu a watan Mayu
2019-04-02 20:10:16 cri

Ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya sanar a yau cewa, kasar za ta karbi bakuncin taron kolin raya fasahohin zamani karo na biyu, wanda zai gudana daga ranar 6-8 ga watan Mayu a Fuzhou, babban birnin lardin Fujian.

Da yake yiwa manema labarai karin haske, mataimakom darektan hukumar kula da harkokin Intanet na kasar Sin, Yang Xiaowei ya bayyana cewa, manufar taron kolin, ita ce samun wata kafa ta gabatar da manufofin kasar Sin kan raya kwaikwayon tunanin dan-Adam, da baje kolin nasarorin da aka cimma wajen tafiyar da harkokin gwamnati ta Intanet da tattalin arziki ta yanar gizo da musayar dabaru da kwarewa a fannin raya fasashohin gina kasar Sin mai fasahar zamani.

Taken taron shi ne "Sabbin fasahohi, sabon ci gaba, sabbin nasarorin da bayanai suka samar", ana kuma saran shirya taruka da baje kolin fasashohin kasar Sin da gasar kirkire-kirkire a yayin taron kolin.

Mataimakin gwamnan lardin Fujian, Zhang Zhinan ya bayyana cewa, masu shirya taron kolin, suna shirin gayyatar baki kusan 1,500. Ya zuwa yanzu, sama da masana 40 daga cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin da cibiyar nazarin aikin injiniya ta kasar Sin da baki daga manyan kamfanonin da suka yi fice a fannin fasaha ne suka ba da tabbacin halartar taron kolin.

Zhang ya ce, fasahohin kwaikwayon tunanin dan-Adam da nau'rori kamar na gane fuska da murya, na biyan kudi ta hanyar tantance fuska, motoci masu tuka kansu, da motoci masu raba kaya marasa matuka ne za a yi amfani da su a lokacin bikin, za kuma a yi amfani da fasahar 5G a manyan wuraren taron kolin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China