in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da hadin gwiwa a fannin binciken sararin samaniya
2019-04-18 10:52:55 cri

Mataimakin darakta a fannin ayyukan injiniya na ma'aikatar lura da binciken sararin samaniyar kasar Sin ta CNSA Mr. Zhao Jian, ya ce kasar sa za ta ci gaba da hadin gwiwa da sauran kasashe, a fannin binciken sararin samaniya.

Jami'in ya ce, Sin za ta bunkasa ayyukan sashen, ta karfafa hadin kai tsakanin kasa da kasa, ta kuma shigar da dabarunta, wajen fadada ayyukan da za su ba da damar cin gajiya daga binciken sararin samaniya.

Zhao Jian, wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai, ya ce za a shirya wani taron masana mai lakabin "warware kalubalen binciken samaniya: da cimma nasarori masu dorewa a fannin" a birnin Changsha, fadar mulkin lardin Hunan tsakanin ranekun 24 zuwa 27 ga watan Afirilun wannan shekara.

Taron, a cewar Mr. Zhao, wanda hukumar CNSA, da hadin gwiwar ofishin MDD mai lura da ayyukan binciken sararin samaniya suka tsara gudanarwa, zai maida hankali ne wajen nazarin dabarun warware matsalolin binciken samaniya, da samar da sabbin damammakin hadin gwiwa, da inganta hadin gwiwar kasa da kasa, tare da ba da gudummawa wajen wanzar da kudurorin ci gaba da aka sanya gaba.

Tun daga shekarar 2016, Sin ta ware ranar 24 ga watan Afirilun ko wace shekara, domin gudanar da bikin ranar samaniya ta kasar, a wani mataki na murnar ranar da kasar ta harba tauraron dan Adam din ta na farko a tarihi, wato ranar 24 ga watan Afirilun shekarar 1970.

Taken shekarar bana dai shi ne "Kaiwa ga muradun binciken sararin samaniya domin cimma moriyar juna cikin hadin gwiwa."(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China