Jami'in ya bayyana hakan ne yayin bikin bude ranar nazarin sararin samaniyar kasar Sin da ya gudana a Changsha, babban birnin lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin.
Zhang ya kuma bayyana cewa, kasar Sin za ta harba tauraron dan-Adam na Change-5, don dawo da samfurorin da ya tattaro zuwa doron duniyarmu a karshen shekarar 2019. Haka kuma kasar ta Sin na harba wani tauraron dan-Adam na farko don gudanar da bincike a duniyar Mars a shekarar 2020. (Ibrahim Yaya)