Da yake karin haske kan cibiyar, mataimakin shugaban sashen kula da al'adu na yankin, Sambo ya ce manufar kafa cibiyar ita ce, yayata al'adun yankin Tibet ta hanyar kamfanonin kirkire-kirkire da irin kayayyakin da suke samarwa.
Alkaluman bincike sun nuna cewa, yawan kamfanonin al'adu a yankin sun haura 6,000, kuma sun dauki ma'aikata sama da 50,000 a karshen 2018. Haka kuma, ribar da suka samu a karshen shekara ta kai sama da Yuan biliyan 4.6 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 683, yayin da suka samu ci gaban da ya kai kaso 15 cikin 100 a shekara.
Sashen kula da al'adun yankin ne dai ya kafa wannan cibiya da nufin cusa sha'awar al'adu ta hanyar samar da horo na kirkire-kirkire da ma baje kolin kayayyakin al'adu da ake samarwa a yankin. (Ibrahim)