in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gama ayyukan yaki da talauci 1493 a yankin Tibet na kasar Sin
2019-03-07 10:55:18 cri

Tun daga shekarar 2016 zuwa 2018, an zuba jari kudin Sin RMB Yuan biliyan 28 da miliyan 692 a yankin Tibet na kasar Sin don gudanar da ayyukan yaki da talauci kimanin 2263, ya zuwa yanzu, an gama ayyukan 1493 daga cikinsu, wadanda suka taimakawa matalauta dubu 210 wajen kawar da talauci ta hanyar raya fannoni.

An yi kokarin raya fannonin shuke-shuke, da kiwon dabbobi, da kera kayayyaki, da cinikayya, da yawon shakatawa, da kuma yin amfani da albarkatu a yankin Tibet, ta hakan an taimakawa dukkan yankin wajen yaki da talauci cikin sauri, da canja aikin yaki da talauci ta hanyar karbar taimako zuwa warware matsalar da kansu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China