Yankin ya kuma samu haraji daga masu yawon bude ido, da ya kai yuan biliyan 1.544, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 230, adadin da ya nuna karuwar kaso 22.3 bisa dari a shekara guda.
Yankin Tibet dai na matukar jan hankulan masu yawon shakatawa, saboda al'adun gargajiya masu kayatarwa, da wuraren ziyara masu ban sha'awa da yake da su. (Saminu Hassan)