Takardar ta bayyana cewa, shekarar 2019, shekaru 60 ke nan da yiwa tsarin demokuradiyya a yankin Tibet na kasar Sin kwaskwarima. Wannan shi ne kwaskwarima mafi girma da aka yiwa tsarin zamantakewar al'ummar yankin Tibet a tarihi, bayan haka, an kawar da tsarin bayi manoma na mulkin malaka'u, da kafa sabon tsarin zamantakewar al'umma. Wannan tsari, ya baiwa jama'a 'yanci, da gudanar da harkokinsu da kansu, da ma kare muradunsa a dukkan fannoni. (Zainab)