in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yankin Tibet ya cika shekaru 60 da samun sauyin demokradiyya
2019-03-29 10:19:24 cri

Wakilai daga kabilu da bangarorin rayuwa daban daban ne suka taru a fadar Potala dake Lhasa a jiya Alhamis, domin murnar cikar yankin Tibet shekeru 60 da samun sauyin demokradiyya.

A watan Maris na 1959 ne, Gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta rushe tsarin masarauta na yankin Tibet tare da 'yantar da sama da bayi miliyan 1, inda ta mayar da su shugabannin al'umma da na kasa.

Da yake jawabi ga taron, shugaban jam'iyyar JKS na yankin, Wu Yingjie, ya ce yankin Tibet ya samu nasarori da dama, sannan ya fuskanci sauye-sauye da dama tun bayan sauyin tsarin gwamnatin ya fara aiki shekaru 60 da suka gabata.

A cewar Wu Yingjie, sauyin tsarin ya kawo karshen mulki irin na sarauta baki daya, tare da rushe mulkin danniya da al'adunta, da kuma 'yantar da mutanen yankin daga bauta.

Ya kara da cewa, cikin shekaru 60 da suka gabata, alkaluma GDP na Tibet sun tashi daga yuan miliyan 174 kwatankwacin dala miliyan 25.9 a 1959, zuwa yuan biliyan 147.76 a bara, wanda ya nuna yankin na samun karuwar kaso 9.5 a kowacce shekara.

Bugu da kari, ya ce an samu gagarumar ci gaba a fannin yaki da fatara. Inda aka fitar da sama da kaso 70 na yankuna da kaso 80 na al'ummar kasar daga kangin talauci. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China