in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cibiyoyin Confucius sun shiga kasashe 149
2018-10-05 15:34:57 cri
Helkwatar cibiyar yada al'adun Sinawa, da koyar da yaren Sinanci ta Confucius, ta ce kawo yanzu, yawan cibiyoyin Confucius dake sassan kasashe 149 ya kai 530, kana cibiyoyin na kunshe da ajujuwa 1,113.

Bisa kididdiga, akwai sama da malamai masu koyarwa a wadannan cibiyoyi har 46,200, wadanda kuma tuni suka koyar da dalibai miliyan 9.

Helkwatar cibiyar wadda ta fidda wadannan alkaluma a ranar bikin ta na shekara, ta hada wata zantawa ta bidiyo tsakanin malaman cibiyoyinta guda bakwai, ciki hadda wadanda ke yankunan Asiya, da Oceania, da Afrika da Turai. Malaman sun nunawa juna dabarun su na koyarwa, da kwarewa a fannin yada al'adu. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China