in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da sakin yarinyar da aka tsare ta a Saudiya bisa zargin safarar miyagun kwayoyi
2019-05-01 15:52:28 cri
Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya, ta tabbatar da sakin yarinyar nan da ba ta san hawa ba balle sauka, mai suna Zainab Aliyu, da mahukuntan kasar Saudiya suka tsare kan laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi.

Babban sakataren ma'aikatar Mustapha Sulaiman, wanda ya sanar da hakan, ya kuma shaidawa manema labarai a Abuja, babban birnin kasar cewa, gwamnatin Najeriyar ta bi dukkan matakai na diflomasiya wajen sakin nata. Ya ce, duk da cewa, an tsare Zainab Aliyu, amma gwamnatin Saudiyar ba ta gurfanar da ita a gaban kuliya ba.

Sulaiman ya ce, an mika ta ne hannun jami'an ofishin jakadancin Najeriya dake kasar Saudiya, Sakin nata ya biyo bayan tattaunawar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Ita dai Zainab Aliyu, daliba ce a jami'ar Maitama Sule dake Kano a yankin arewa maso yammacin Najeriya, ta kuma je aikin umra ne a watan Disamban shekarar 2018, lokacin da mahukuntan kasar ta Saudiya suka tsare ta bisa zargin cewa, akwai kwayar Tramadol a daya daga cikin jakanta dake dauke da sunanta, kwayar da mahukunta kasar suka haramta shigo da ita cikin kasar. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China