in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya ta sabunta kira da yaki da zazzabin cizon sauro yayin da ake tsaka da fama da gibin kudi a bangaren
2019-04-26 09:35:31 cri

Daruruwan jama'ar Nijeriya ne suka yi dogon tattaki jiya a birnin Abuja, domin gangamin yaki da cutar zazzabin cizon sauro wato malaria a kasar.

Ma'aikatar lafiya ta kasar da kungiyoyin al'umma da dama ne suka shirya tattakin da ya kunshi yara da manyan jami'an gwamnati, a wani bangare na shirye-shiryen ranar yaki da cutar Malaria ta duniya, wadda ke gudana a duk ranar 25 ga watan Afrilun kowacce shekara.

Masu tattakin sun jure zafin rana domin ilmantar da jama'a a kasar dake yammacin Afrika, hanyoyin yaki da cutar malaria.

Taken bikin na bana shi ne "kawar da malaria zai fara daga ni"

A cewar rahoton yaki da malaria na duniya, har yanzu, cutar malaria kalubale ne ga lafiyar al'umma a kasar mafi yawan jama'a a Afrika, kuma kasa ce ke da da kaso 25 bisa dari na matsalar malaria a duniya.

Ministan lafiya na kasar Isaac Adewole, ya ce Nijeriya na bukatar karin kudi domin cimma burin rage barkewar cutar da mace-macen da take haifarwa da a kalla kaso 40 ya zuwa shekarar 2020.

A cewar ministan, da ranar yaki da malaria ta duniya, ta samar da damar da ta dace na bitar dabarun da aka yi amfani da su, da kara matse kaimi da nufin rage matsin da kasar ke fama da shi dangane da cutar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China