in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojan Najeriya ta tabbatar da kashe 'yan bindiga 6 a arewacin Zamfara
2019-04-23 09:18:22 cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, dakarunta sun yi nasarar kashe 'yan bindiga masu dauke da makamai guda 6, yayin wasu hare-hare da sojojin suka kaddamar a karshen mako a jihar Zamfara dake arewacin kasar.

Mai magana da yawun rundunar sojojin kasar Sagir Musa, shi ne ya sanar da hakan, Yana mai cewa, an kuma kama masu taimakawa 'yan bindigar da bayanai sirri guda 18, ciki har da wani dagaci, a lokacin da suka mamaye kauyuka hudu a kananan hukumomin Anka da Gusau a jihar ta Zamfara dake yankin arewa maso yammacin kasar ta Najeriya.

Musa ya ce, sojojin sun kuma yi nasarar kwato makamai a hannun 'yan bindigar.

A farkon watan nan ne dai, rundunar sojojin Najeriyar, ta kaddamar da hari ba kakkautawa kan kungiyoyi masu dauke da makamai a jihar, a wani mataki da sojojin ke dauka na kawar da 'yan bindiga da munanan ayyuka a jihar ta Zamfara. Musamman yankin arewa maso yammacin kasar baki daya, inda ake ta samun rahotannin satar shanu da fashi da makami.

A 'yan watannin nan, Jihar Zamfara da ma jihar Kaduna mai makwabtaka, sun sha fuskantar jerin hare-haren kungiyoyin masu dauke da makamai.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China