in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya sanya hannu kan dokar sabon mafi karancin albashi
2019-04-19 09:27:58 cri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sanya hannu kan dokar sabon mafi karancin albashi na kudin kasar Naira 30,000, kwatankwacin dalar Amurka 83.33 a duk wata, ga ma'aikatan hukuma da na kamfanoni, ban da kamfanonin da ma'aikatan su ba su kai 25 ba.

Kafin hakan, kudurin dokar ya samu amincewa a zauren majalissar wakilan kasar gabanin babban zaben kasar na watan Fabarairu.

Da yake tabbatar da hakan, babban mataimakin shugaban kasar game da harkokin majalissar dokoki Ita Enang, ya ce za a fara aiwatar da sabon tsarin albashin ne nan take.

A cikin watan Nuwambar bara ne dai kungiyar kwadago ta Najeriya ta shiga wani yajin aiki na sai baba ta gani, domin matsawa gwamnati lamba, sakamakon zargin da ta yi cewa, gwamnatin ka gaza wajen cika alkawarin da ta dauka na tabbatar da karin albashi. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China