in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Nijeriya ta lashi takobin sake sada 'yan matan da aka sace da iyayensu
2019-04-26 10:51:54 cri

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatinsa za ta yi dukkan abun da ya kamata domin taimakawa sauran 'yan matan da aka sace sake saduwa da iyalansu.

Muhammadu Buhari, ya bayyana jiya a Maiduguri, babban birnin jihar Borno na yankin arewa maso gabashin kasar, wadda ke fama da rikici cewa, a matsayinsa na shugaban kasa, dan Nijeriya, kuma uba, yana jimami kamar kowanne dan kasar da aka sace wani makusancinsa, a don haka, gwamnati za ta yi dukkan abun da ya kamata don ganin wadannan 'yan mata sun sadu da iyayensu.

Shugaban ya ce zaman lafiyar da aka samu, ya ba gwamnatin jihar Borno damar aiwatar da ayyuka a bangarorin samar da gidaje da ginin tituna da bangaren harkokin gona da masana'antu da kuma ilimi.

Shugaban ya kara da cewa, yadda gwamnatin jihar ta mayar da hankali kan bangaren ilimi abun ne mai muhimminci, duba da kalubalen mayakan Boko Haram, wadanda akidarsu ke adawa da ilimin boko.

Shugaban na Nijeriya, ya ce ya yi farin ciki da ganin an ware wasu daga cikin sabbin makarantun ga ilimin yara mata kacokan, yana mai cewa akwai hikima a cikin matakin, wanda kuma martani ne da ya dace da akidar Boko Haram. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China