in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojoji a Najeriya sun kashe 'yan bindiga a kalla 10 a Zamfara
2019-04-24 10:43:18 cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, rundunar sojojin saman kasar, sun yi nasarar kashe a kalla 'yan bindiga masu dauke da makamai guda 10, yayin wani hari ta sama da suka kaddamar a maboyarsu a jihar Zamfara dake yankin arewa maso yammacin kasar.

Da yake karin haske kan hakan, mai magana da yawun rundunar Ibikunle Daramola, ya bayyana cewa, 'yan bindigar suna sake taruwa ne a dajin Sububu dake jihar a ranar Litinin, lokacin da sojojin suka amsa bukatar taimakon sanya ido ta sama daga takwarorinsa na kasa.

Bugu da kari, rundunar sojojin saman kasar, ta tura jiragen yaki kirar Alpha guda biyu da jirgi mai saukar ungulu dake kai hari, domin taimakawa tare da kai hari kan maboyar 'yan bindigar da aka gano a karamar hukumar Shinkafi da dazukan Sububu da Dumburum da kewaye.

Ya ce, daya daga cikin jiragen yakin su, ya gano gungun 'yan bindigar a dajin Sububu. Nan da nan ne kuma, 'yan bindigar suka kaiwa jirgin hari, suka kuma arce.

Jami'in ya ce, dakarunsu sun mayar da martani, inda suka jikkata 'yan bindiga da dama, suka kuma arce da raunukan harbin bindiga a jikinsu. Ya ce, sojojin za su hada kan sojojin kasa da sauran hukumomin tsaro, da ci gaba da kai hare-haren da suke kaddamarwa da nufin kawar da 'yan bindigar daga yankin arewa maso yammacin kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China