in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya taya sarki Naruhito na Japan murnar darewa karagar mulki
2019-05-01 15:01:31 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya taya sarki Naruhito na Japan murnar darewa karagar mulki, cikin wani sako da shugaban ya aike ga sabon sarkin a Larabar nan.

Cikin sakon, Xi ya ce Sin da Japan makwafta ne na kusa da suka jima suna kawance. Don haka ya dace su yi hadin gwiwa wajen wanzar da zaman lafiya da ci gaba, domin cimma nasarar samun makoma mai haske ta hadin kai tsakanin su.

Kaza lika a dai wannan rana, shugaba Xi ya gabatar da sakon gaisuwa da fatan alheri ga sarki mai murabus Akihito, mahaifi ga sabon sarkin da ya dare karagar mulki. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China