Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a gun taron taron cika shekaru 100, da gudanar da zirga-zirgar kishin kasa cewa, ya kamata kwamitocin jam'iyyar kwaminis ta Sin da gwamnatocin kasar da kuma bangarori daban daban na kasar su saurari ra'ayoyin matasa game da ayyukan jam'iyyar da gwamnatin kasar.
Ya ce, ya kamata a taimakawa matasa wajen daidaita matsalolinsu na samun ayyukan yi, da yin kirkire-kirkire, da kafa kamfanoni da saurnasu, da sa kaimi gare su da fahimci duniya da yanayin da kasar ake ciki. (Zainab)