Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, shi ne ya bayyana hakan, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da janyewar kasarsa daga yarjejeniyar cinikayyar makamai ta ATT a ranar 26 ga watan Afrilu, yarjejeniyar dake sanya ido kan cinikayyar makamai ta kasa da kasa da kandagarki da magance yin cinikayya ba bisa ka'ida ba, da canja akalar makamai, ta hanyar kafa ma'aunin ingancin kasa da kasa game da canzawa makamai matsuguni.
Geng ya ce, kasar Sin tana goyon bayan dalili da ma manufar kafa yarjejeniyar, kuma tana halartar tarukan da abin ya shafa a matsayin 'yar kallo. Bugu da kari, kasar Sin tana duba yiwuwar shiga yarjejeniyar. (Ibrahim)