in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya gabatar da shawarwari kan yadda za a tafiyar da harkokin kasa da kasa
2019-03-26 11:43:26 cri
Mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gabatar da shawarwari guda uku kan yadda za a tafiyar da harkokin kasa da kasa bisa nuna daidaito, tsari, da kuma yadda tarihi ya nuna.

Wang wanda ke yiwa shugaba Xi Jinping rakiya a ziyarar aikin da ya kai kasar Faransa, ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a bikin dandalin tafiyar da harkokin kasa da kasa da kasashen Sin da Faransa suka shirya tare.

Ya kuma yi kira da a rika tattaunawa ba tare da wata rufa-rufa ba, da zurfafa musaya da koyon al'adu da tunanin juna tsakanin kasashe, da hikima da cimma matsaya ta yadda za a inganta tafiyar harkokin kasa da kasa.

Jami'in na kasar Sin, ya kuma bayyana bukatar yin hadin gwiwa, da akidar samun moriya tare da alakar mutunta juna, yana mai kira ga kasashen Sin da Faransa da su zurfafa yin tattaunawa a tsakaninsu a fannonin da za su kai ga hadewar juna, yiwa kungiyar cinikyayya ta duniya gyaran fuska da ma yadda ake tafiyar da harkokin intanet.

Wang Yi ya kuma yi kira a warware sakamakon moriyar juna da ta bangarorin da dama ta hanyar da ta kamata, ta yadda al'ummomin sassan kasashe daban-daban da ma daukacin bangarorin rayuwa za su ci gajiyar yadda ake tafiyar da harkokin kasa da kasa.

A nasa jawabin ministan harkokin wajen kasar Faransa, Jean Yves Le Drian, ya cewa, Faransa na goyon bayan tsarin MDD, ta kuma yi imani da cudanyar kasashen duniya.

Ya kara da cewa, turai da Asiya da shawarar ziri daya da hanya daya, suna taimakawa juna, kana bangaren Faransa, yana goyon bayan hadewar sassan biyu da hada kai da Sin game da ayyukan da suka shafi sassan biyu. (IbrahimYaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China