Geng Shuang wanda ya bayyana hakan a Talatar nan yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ya ce a shirye kasar Sin take ta taimakawa kasashen da wannan ifta'i ya shafa daidai karfinta kuma kamar yadda gwamnatocin kasashen uku suka bukata.
Ya ce, gwamnatin kasar Sin, tana jajantawa kasashen Mozambique da Malawi da Zimbabwe bisa ga asarar rayuka da dukiyoyin da mahaukaciyar guguwar ta haddasa, tana kuma mika ta'aziya ga iyalan wadanda suka mutu tare da fatan samun sauki cikin hanzari ga wadanda suka jikkata.
Kimanin mutane 84 ne aka ba da rahoton sun mutu a Mozambique, 56 a kasar Malawi sai kuma mutane 98 a kasar Zimbabwe.
Sai dai shugaba Filipe Nyusi na Mozambique ya bayyana a jiya Litinin cewa, yawan wadanda suka mutu a kasarsa zai haura 1,000. (Ibrahim Yaya)