in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin: Karar da kamfanin Huawei ya shigar tana bisa turba
2019-03-08 09:11:23 cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya ce, karar da kamfanin Huawei ya shigar kan gwamnatin Amurka bisa doka, ya yi shi ne da nufin kare 'yanci da martabarsa.

A yau Alhamis ne kamfanin na Huawei ya shigar da gwamnatin Amurkar kara, saboda haramtawa hukumomin tarayyar kasar amfani da kayayyakin kamfanin.

Sai dai kuma kamfanin Huawei ya bayyana yayin wani taron manema labarai da ya kira a Shenzen dake lardin Guangdong, cewar ya karyata zargin da gwamnatin Amurkar ta yi na barazanar tsaro kan kayayyakin kamfanin ba tare da Amurka ta gwada kayayyakin nata ba.

Kamfanin ya shigar da karar ce a gaban kotun gundumar Plano dake jihar Texas. Inda kamfanin ya yi korafin cewa, gwamnatin Amurka ta haramtawa hukumomin tarayyar kasar amfani da kayayyaki da ma hidimomin kamfanin, haka kuma ta haramta yin wata mu'amala ta kudi ko rance ga duk wanda ya sayi kayayyaki ko hidimar kamfanin.

Kamfanin Huawei dai, yana kan gaba wajen bullo da fasahar 5G, kana kamfanin yana sahun gaba wajen yin gogayya da manyan kamfanoni irinsu su Apple.

Bayanai na cewa, duk da barazar tsaron da Huawei ke fuskanta a wasu kasuwanni, kamfanin na kara samun kwangiloli a aikinsa na 5G. Inda ya bayyana a taron manema labarai na baya-bayan cewa, ya zuwa yanzu, ya samu kwangiloli sama da 30 na fasahar 5G a kasuwannin ketare.

Matakin gwamnatin Amurka na haramta amfani da tsarin NDDA ya hana kamfanin samar da fasahar 5G ta zamani ga abokan hulda a Amurka, matakin da zai jinkirta amfani da fasahar ta 5G. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China