in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu manyan jami'an diflomasiya sun ziyarci yankin Xinjiang
2019-03-12 09:30:51 cri
Rahotanni daga yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa dake nan kasar Sin na cewa, wasu manyan jami'an diflomasiya daga kasashe 7 gami da kungiyar kasa da kasa sun ziyarci yankin daga 28 ga watan Fabrairu zuwa 2 ga watan Maris bisa gayyatar gwamnatin yankin.

Yayin ziyarar, jami'an diflomasiya daga kasashen Myanmar, da Aljetiya da Morocco, da Vietnam, da Hungary, da Greece, da Singapore gami da wata tawaga daga kungiyar kasashen Larabawa dake nan kasar Sin, sun ziyarci sassa daban-daban dake yankin, sun kuma tattauna sosai da mazauna wuraren.

Jami'an sun bayyana cewa, sun ji dadin yadda mazauna yankin ke mu'amala da jama'a da yadda kabilu daban-daban dake yankin suka hada kansu da ma irin nasarorin da yankin ya samu a fannin inganta rayuwar jama'a.

A jawabinsa shugaban tawagar kungiyar kasashen Larabawa dake nan kasar Sin Mahmoud Hassan Elamin, ya ce, ziyarar ta ba su damar kara fahimtar yankin, yana mai cewa, ci gaban yankin, zai baiwa kowa da kawo damar amfana dai-dai gwargwado. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China