Lu Kang ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani game da korafin da aka gabatar na ganin Amurkar ta dawowa da kasar Sin kayayyakinta na tarihi.
Kasar Amurkan dai ta sanar da dawo da kayayyakin tarihin kasar Sin 361 a yayin wani biki da ya gudana jiya Alhamis a dakin adana kayayyakin tarihi na Eiteljorg dake Indianapolis na jihar Indiana.
Jami'in na kasar Sin ya ce, alaka a fannin kare kayayyakin tarihi abu ne mai muhimmanci kan alakar al'ummomi, al'adu da musaya tsakanin kasashen Sin da Amurka. Kana kasar Sin za ta hada kai da Amurka don karfafa musaya da hadin gwiwa a fannin kare kayayyakin tarihi da ba da babbar gudummawa a kokarin da ake na kare al'adun gargajiya a duniya. (Ibrahim)