in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta saukaka biyan kudin cinikayya ta intanet daga kasashen waje
2019-04-30 10:35:03 cri

Hukumar kula da musayar kudi ta kasar Sin, ta fitar da wasu ka'idojin saukaka biyan kudin cinikayya ta intanet da aka yi daga kasashen waje.

A cewar ka'idojin, an ba cibiyoyin biyan kudi damar ba masu sayayya hidimomin da suka shafi biyan kudi ta intanet ta hannun bankuna, karkashin tsarin bayanan hada-hadar kudi tsakanin al'ummar kasar da kasashen ketare, bisa dogaro da bayanan hada hadar kudi ta intanet da suka dace.

Za kuma su iya ba Sinawa hidimomin musayar kudi domin sayayya daga ketare ko biyan kudin makaranta ko yawon bude ido.

Domin cimma bukatun dake karuwa a fannin sayayya daga ketare ta intanet, kasar Sin ta kaddamar da hidimomin musayar kudi na gwaji, ta hannun cibiyoyin biyan kudi a biranen Shanghai, Beijing, Chongqing, Shenzhen da ma wasu biranen lardin Zhejiang a 2013, a kuma shekarar 2015 ne ta fadada zuwa fadin kasar baki daya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China