Kabilar Dulong na daya daga cikin kabilun kasar Sin da al'ummarsu ba su da yawa, kuma suna zaune ne a yankin Nujiang da ke lardin Yunnan na kasar. "Menzu" shi ne salon wakar gargajiya na kabilar, kuma al'ummar kabilar Dulong su kan yada tatsuniyoyinsu da almara da sauran batutuwan kabilar daga zuriya zuwa zuriya yayin da suke rera wakar. Sai dai sakamakon ci gaban zamani, salon wakar na dab da bacewa, yanzu mutane kalilan ne ke iya rera wakar.
Malama Ken Yuzhen mai shekaru 66 a duniya na daga cikin wadanda suka gaji fasahar salon wakar na lardin Yunnan, kuma ta kan shirya wasanni don fadakar da al'ummar kan salon wakar. A shekarar 2015, ta fara koya wa wasu dalibai 5 salon wakar. Ta ce, za ta iya bakin kokarinta wajen ganin ta ci gaba da yada salon wakar, ta yadda ba za ta bace ba.