in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kara zuba jarin sama da dala biliyan 3.7 ga kasashen dake aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" a farkon watannin ukun bana
2019-04-16 20:16:30 cri
Alkaluman da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar yau sun nuna cewa, daga watan Janairu zuwa Maris din bana, adadin jarin da kasar Sin ta zuba a kasashen ketare ya zarce dala biliyan 25. A watan ne Maris, yawan jarin da kasar Sin ta zuba kai-tsaye a ketare ya kai dala biliyan 9.55, wanda ya karu da kashi 10 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. Mataimakin shugaban sashin kula da harkokin hadin-gwiwa na ma'aikatar kasuwancin Sin Han Yong ya ce, Sin na zuba jari a kasashen waje yadda ya kamata.

Han ya ce, a farkon watanni uku na shekarar da muke ciki, kamfanonin kasar Sin sun kara zuba jari a wasu kasashe 49 dake cikin shawarar "ziri daya da hanya daya", wanda ya kai dala biliyan 3.76, adadin da ya karu da kashi 4.2 bisa dari bisa na makamancin lokacin bara. Kana, kamfanonin Sin sun kuma rattaba hannu kan wasu sabbin kwangilolin ayyuka da darajarsu ta kai dala biliyan 30.48 a kasashen da abun ya shafa, wanda ya dauki kashi 60.2 bisa dari na jimillar darajar kwangilolin da suka daddale.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China